Bauchi jaha ce dake yankin Arewacin Najeriya tana yankin Arewacin gabashin Najeriya an kirkiri jihar Bauchi ne a watan Fabrairun shekarar ta 1976 daga tsohuwar jihar Arewa maso Gabas ta gwamnatin Janar Murtala Mohammed. Asali ta hadane da yankin Gombe, wadda ta zama jiha ta daban a shekarar 1996. Tana da kananan hukumomi Ashirin 20. Babban birninta shi ne Bauchi.
Jihar Bauchi tana yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, tana da fadin murabba'in kilomita 45,837. Jihar Bauchi tana iyaka da Kano da Jigawa daga arewa sai Yobe da Gombe daga gabas sai jihar Kaduna ta yamma da Filato da Taraba a kudu.
Gaba daya yankunan yammacin jihar da arewacin kasar suna da tsaunuka, da duwatsu. Hakan ya faru ne sakamakon kusancin jihar da tsaunukan Jos ta jihar Plateau da kasar Cameroun.
Jihar Bauchi na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya da suka mamaye yankunan ciyayi guda biyu, wato Sudan Savannah da Sahel Savannah. Manyan koguna guda biyu ne suka ratsa jihar, kogin Gongola da Hadejia. Yanayin yanayin jihar Bauchi yana da zafi sosai a watannin Afrilu da Mayu, yayin da Disamba da Janairu ne watanni mafi sanyi.
Jihar Bauchi na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya da suka mamaye yankunan ciyayi guda biyu, wato Sudan Savannah da Sahel Savannah. Manyan koguna guda biyu ne suka ratsa jihar, kogin Gongola da Hadejia. Yanayin yanayin jihar Bauchi yana da zafi sosai a watannin Afrilu da Mayu, yayin da Disamba da Janairu ne watanni mafi sanyi.
Jihar Bauchi tana da ƙabilu masu yawa, wanda sun kai ƙabilu 55 da suka haɗa da Fulani, Gerawa, Sayawa, Jarawa, Kirfawa, Turawa Bolewa, Karekare, Kanuri, Fa'awa, Butawa, Warjawa, Zulawa, BoyawaMBadawa. Amma Fulani su ne ƙabila mafi Yewa a Jahar,inda suka mamaye kananun hukumomi irinsu Toro, jama'are, giade, darazo, katagum, misau, Alkaleri, dambam, da dai sauran su. Wannan yana nufin cewa suna da asali,da tsarin sana'a, da sauran abubuwa da yawa waɗanda ke cikin kasancewar al'ummar jihar.
An samo Sunan garin Bauchi ne daga sunan wani Baushe wanda ya kasance jajirtaccen mafarauci a zamaninsa. Baushe shine ya fara zama a Bauchi kafin zuwan Malam Yakubu Sarkin Bauchi na farko. Bauchi a cewar masu fassarar Hausa na farko na nufin “babu wata dabba da ta tsira daga tarko da kibiryar Baushe”.
Akwai kamanceceniyar al'adu a tsakanin kabilun jihar, ayyukan sana'a, bukukuwa, sutura da kuma yawan mu'amalar ƙabilanci musamman wajen zaman aure da tattalin arziki. Wasu daga cikin ƙabilun suna da alaƙar barkwanci da ke tsakanin su, misali; Fulani da Kanuri, Jarawa da Sayawa, da sauransu.
Jihar Bauchi jihar noma ce. Sunada Faɗin ƙasa mai albarka hakan yasa yana ƙara fa'ida ga kayan amfanin gonar da suke samarwa, waɗanda suka haɗa da masara, shinkafa, gero, gyada. Ana yin noma da tallafawa ta hanyar amfani da madatsun ruwa kamar dam na Balanga da sauransu. Haka nan ana kiwon shanu da sauran dabbobi a jihar.
Haka kuma jihar tana da masana’antun da suke samar da kayayyakin Amfanin Al'umma na yau da kullum.
Jihar Bauchi na da albarkar wuraren yawon bude ido da dama. Jihar Bauchi tana da wurin ajiyar Dabbobi na Yankari (mafi girman kiwo a Afirka ta Yamma), Premier Game Reserve, Rock Paintings a Goji da Shira, Gidan Tarihi na jiha
Shehu Azare Park
Tunga Dutse
Wikki Warm Springs
Yankari National Park (Game Reserve).
Amanya Festival
Bikin Fasaha da Al'adu na Jahar Bauchi
Idin kaciya na mutanen Gezawa
Durbar Festival
Kokowa and Dambe Festival
Lake Efi Fishing Festival
Bikin Al'adun Yankari
Bikin Daba (Durbar) babban abin jan hankali ne na shekara-shekara[1]
SHUGABANNIN GANANON HUKUMUMIN JIHAR BAUCHI.
Garamar Hukumar Dass: Ado Mai goro (Shugaba) da Yusuf wakili (Mataimaki)
Garamar Hukumar Gamawa: Nasiru Bakora (Shugaba) da Salisu Dahiru (Mataimaki)
Garamar Hukumar Ganjuwa: Muhammad Idris (Shugaba) da Ibrahim Shehu Baba (Mataimaki)
Garamar Hukumar Giade: Abubakar Nawaila (Shugaba) da Abdullahi Idris (Mataimaki)
Garamar Hukumar Itama/Gadau: Abubakar Bello (Shugaba) da Yakubu sadiku (Mataimaki)
Garamar Hukumar Jama'are: Inuwa Moisha (Shugaba) da Saleh Muhammad (Mataimaki)
Garamar Hukumar Katagum: Umar Hassan (Shugaba) da Abdullahi Datti (Mataimaki)
Garamar Hukumar Kirfi: Muhammad Tukur Adamu (Shugaba) da Muhammad Bashar (Mataimaki)
Garamar Hukumar Misau: Salisu Husaini (Shugaba) da Sallau Garba Tela (Mataimaki)
Garamar Hukumar Ningi: Ibrahim Zubairu Mato (Shugaba) da Muhammad lawan (Mataimaki)
Garamar Hukumar Shira: Babangida Mohammed (Shugaba) da Adamu Usman (Mataimaki)