Sardauna Memorial College
![]() |
---|
Sardauna Memorial College (SMC) wacce aka fi sani da suna Sheikh Sabah College, Kaduna. Makarantar sakandare ce a kaduna wanda Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah ya kafa a jihar Kaduna yayin ziyara, bayan rasuwar Firayim Ministan Arewacin Najeriya Sir Ahmadu Bello makarantar ta canza sunan ta zuwa Sardauna Memorial College, ga abin da yake a yau kamar yadda Sardauna Memorial College (SMC). Ana gudanar da sallar juma'a a Massalacin Wanda kungiyar izala take daukar ragamar massalacin da gudanar da da'awa da dai sauran su.
Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]
![Sardauna memorial collage](http://chped.net/https/upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/d/d6/Sardauna_Memorial_College.jpg/220px-Sardauna_Memorial_College.jpg)
Cibiyar Inshorar da Ma'aikata ta Najeriya wacce ake kira (NDIC) ta ba da gudummawar miliyan N24.9 na Kwalejin Sardauna Memorial (SMC) Kaduna, don samar da e-libarary.
Alumni[gyara sashe | gyara masomin]
![Sheikh saba](http://chped.net/https/upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/3/35/Sheikh_Sabah_Memorial_Mosque_SMC_06.jpg/220px-Sheikh_Sabah_Memorial_Mosque_SMC_06.jpg)
Tsofaffin daliban makarantar tana da wata kungiya da ake kira Sardauna Memorial College Old Boys Association, SAMOBA, Wadannan sunayen manyan mutane ne dasuka halarta makarantan
- Ahmad Abubakar Gumi
- Muhammadu Lawal Bello
- Jika Dauda Halliru
- Shehu Ladan
- Usman Shehu Bawa
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
![](http://chped.net/https/upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/a/a4/Sardaunan_Memorial_College_kaduna.jpg/220px-Sardaunan_Memorial_College_kaduna.jpg)
Daliban SMC ne suka fara cin gasar kwallon kafa na makarantun sakandare na duniya a ƙasar Finland.