Jump to content

Samfuri:Kanun labarai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
  • Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai rika tuntubar juna da aiwatar da abubuwan da aka cimma bayan, kammala taron inganta zaman lafiya da tsaro a yankin da aka gudanar a Katsina.
  • Shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tchani ya gana da tsoffin shugabannin kasar Bénin Nicephore Soglo da Boni Yayi a Yamai
  • Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu ya ce zai tuntubi gwamnonin jihohi kafin yanke shawarar karshe game da sabon tsarin albashi
  • A jamhuriyar kasar Mali, faraministan kasar Choguel Kokalla Maiga, ya gana tare da Abdou Adamou jakadan kasar Nijar dake Mali a ranar jiya 24 ga watan Junin shekarar 2024 a fadar faraministan kasar Mali dake birnin Bamako.
  • Julian Assange da ya kirkiro shafin kwarmata bayanai na WikiLeaks, ya amsa aikata laifi guda na keta dokar cin amanar kasa a wata babbar kotun tarayya dake Saipan, babban birnin Arewacin Tsibirin Mariana, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da ya cimma da ma’aikatar shari’a ta Amurka, domin kaucewa kara zaman kaso, tare da kawo karshen shari’ar da aka dauki shekaru ana yi.