Jump to content

Azumi a kasar Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Azumin watan Ramadan ibada ce ta wajibi ga dukkan musulmai baki daya, Azumin watan Ramadan ginshiki ne daga cikin ginshiken Addinin Musulunci, wanda cikar musuluncin musulmi bai cika sai da shi, Shari'ah ce wadda Allah (SWT) ya yi umarni da yinta a cikin Al'qur'ani mai Girma inda yake cewa "An wajabta yin azumi a gareku kamar yanda aka wajabta shi ga wadanda suke gabaninku domin ku zamo masu tsoron Allah". Azumin watan Ramadan ibada ce wadda ake kamewa daga barin ci ko sha ko saduwa da iyali tsawon yini daga hudowar Alfijir zuwa Faduwar Rana (Magrib). Ana yin shi ne na tsawon kwanaki 30 ko 29 a cikin watan Ramadan wanda shine wata na Tara a jerin watannin musulunci. [1]

Azumi a kasar Hausa[gyara sashe | gyara masomin]

Musulmai a kasar Hausa suna azumi kamar kowace al'ummar musulmin duniya kamar yanda aka shar'anta masu suna daukar azumin ne bisa umarnin Sarkin Musulmi ta hanyar ganin jimjirin wata. Idan Masarautar Daular Musulunci tayi umarnin fara duban watan Ramadan Yara da Matasa da sauran al'umma suna fitowa suyi dafifi domin duban watan tun daga lokacin da rana tazo faduwa har zuwa gari ya fara duhu, bayan an sami sanarwa yara zasu fito suna murna suna wake wake na gargajiya na ganin watan azumin.[2] Iyalai suna fara shirye shiryen kayan azumi tun kafin shigowar watan, tsare tsaren abincin Sahur dana buda baki, Abinci kala-kala, daban-daban na gargajiya ake shiryawa. A wasu sassa musamman kauyuka makada masu amfani da ganga ake umarta da su agaya cikin mutane domin su sanar dasu cewa an ga wata Sarkin Musulmi yabada sanarwar a dauki azumi. Ramadan wata ne na falala wanda daukacin musulmai musamman a kasar Hausa suke dukufa wajen Salloli da bada Sadakoki da neman yarda da gafarar Allah SWT, Masallatai da dama suna shirya karatun Tafsirin Al'qur'ani mai Girma.

Malamai da dama sukan shirya tarurruka domin fadakarwa da zaburar da jama'a wajen zage damtse wurin yin Bauta da addu'oi da dagewa kwarai da gaske wajen yin bauta. [3] Bayan Azumin goma Farko, yara da matasa sukan yi wasa na gargajiya da ake kira da 'Tashe'. Tashe wasa ne na gargajiya wanda ya kunshi raye-raye, wakokin grgajiya, da barkwanci domin a nishadantar da mutane, masu yin wasan tashe suna zagayawa gida gida suna yin wasan ana basu kudi na tukuici, wasu kuma suna zagayawa cikin kasuwanni da rana suna yin wassanin , wannan wasa na tsahe ana yinsa ne na tsawon kwanaki goma. [4] A Goman karshe na watan Ramadan, kamar yanda yazo a Al'qur'ani mai girma cewa ana dacewa da daren 'Laylatul Qadri' a wannan ranakun a cikin mara, mutane da yawa suna dafifi wajen fita zuwa masallatai domin yin sallar dare ta Tahajjud, wasu kuma suna tarewa a manyan masallatai musamman na juma'a su dukufa dayin ibada. Kaha zalika wa wannan kwanaki ne Mutane suke shagala wajen ganin sunyi dunkuna sababbi domin Sallar Idi, wanda wani biki ne da ake gudanarwa bayan kammala azumin watan Ramadan. Ana samun sanarwa da umarni daga fadar Sarkin Musukmi cewa sabon wata ya tsaya don haka watan Ramadan ya kare kowa zai aje azumi don gobe take Sallah. [5]

Al'adun bahaushe lokacin Azumi[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.britannica.com/topic/Ramadan
  2. https://www.taghribnews.com/en/news/103164/fasting-of-ramadan-in-hausa-land-northern-nigeria
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-29. Retrieved 2023-03-29.
  4. https://www.taghribnews.com/en/news/103164/fasting-of-ramadan-in-hausa-land-northern-nigeria
  5. https://www.taghribnews.com/en/news/103164/fasting-of-ramadan-in-hausa-land-northern-nigeria